Shugaban kasa Tinubu ya rantsar da Darma a matsayin minista

Darma sworn in by Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya rantsar da Dr Muttaqha Rabe Darma a matsain sabon ministan gidaje na kasar.

Dr Darma  dan asalin jihar Katsina  ya maye gurbin Ahmed Musa Dangiwa, wanda ya yi murabus a baya-bayan nan.

An rantsar da sabon ministan ne a wani kwarya-kwaryar biki da aka gudanar a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa ga Dr Darma, saboda tarihin abubuwan da ya gabatar a baya.

Dr Darma babban malamin jami’a ne kuma gogaggen ma’aikacin gwamnati masani a bangaren ci gaba. Ya yi karatu a Jami’ar Bayero ta Kano da Jami’ar Benin da Jami’ar Liverpool da kuma Jami’ar Atlantic International inda yayi digirin shi na uku.

Darma ya rike mukamai da dama a jiharsa ta Katsina ciki har da kwamishinan ayyuka da sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here