Gwamnan Kano ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu a hatsarin mota da ya kashe sama da mutane 30 a Kano

Abba Kabir Yusuf 750x430

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini da jajantawa ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru da sassafe a yankin Kwanar Barde da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane talatin ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin, wanda ya jefa al’umma cikin jimami da alhini, musamman ganin yadda lamarin ya faru ba zato ba tsammani.

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya auku ne da sassafe a ranar Lahadi, inda wata babbar mota dauke da kaya da ke kan hanyarta ta zuwa Gujungu ta yi hatsari, wanda ake danganta faruwar sa da tuƙi cikin ganganci ba tare da kiyaye dokokin hanya ba.

Hatsarin ya jikkata fasinjoji da dama, inda da yawa daga cikinsu suka samu munanan raunuka, kuma aka garzaya da su asibitoci daban-daban domin samun kulawar gaggawa a faɗin jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu, ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hatsarin a matsayin abin tausayi da babban rashi, ba ga iyalan da abin ya shafa kaɗai ba, har ma da daukacin al’ummar jihar Kano.

Gwamnan ya roƙi Allah Ya jikan waɗanda suka rasu, ya kuma bai wa iyalansu juriyar wannan babban rashi, tare da addu’ar samun sauƙin warkewa ga waɗanda ke karɓar magani a asibitoci.

Sannan ya umarci ma’aikatar lafiya ta jihar Kano da ta tabbatar an bai wa dukkan waɗanda hatsarin ya rutsa da su kulawar lafiya kyauta kuma ba tare da ɓata lokaci ba, tare da gargaɗin direbobi musamman na manyan motoci da su guji tuƙi cikin ganganci tare da bin ƙa’idojin zirga-zirga domin kauce wa afkuwar irin wannan masifa a nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here