Gidauniyar Mangal ta duba masu lalaurar ido 18,000 a Katsina

WhatsApp Image 2026 01 03 at 07.55.14 750x430

Akalla marasa lafiya 18,000 da ke fama da cututtukan ido daban-daban sun amfana da maganin ido da tiyata kyauta daga gidauniyar Mangal tun daga shekarar 2016.

Wani mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar, Hussaini Kabir, ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin fara aikin tiyatar ido na zangon karshe na shekarar 2025 a jihar Katsina.

Ya bayyana cewa a shekarar 2025 kadai, mutanen da suka amfana sun kai kimanin 7,000 daga jihar Katsina, jihohin makwabta da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar.

Kabir ya kara da cewa an fara tantance marasa lafiyar ne tun makonni biyu da suka gabata, inda aka raba magunguna kyauta da tabarau na likitanci ga masu bukata.

Ya kuma bayyana cewa duk marasa lafiyar da ke bukatar tiyata, gidauniyar ce ke daukar nauyin kwanciya da kula da su a asibiti gaba daya, inda ya ce kimanin mutane 2,000 aka tantance a wannan aikin da ke gudana.

Kabir ya jaddada kudurin gidauniyar na ci gaba da inganta samun kiwon lafiya ga jama’a a matsayin wani bangare na nauyin da take dauka na taimakon al’umma.

Wani kwararren likitan ido, Ahmad Hamza, ya bayyana cewa yawancin marasa lafiyar da aka duba an gano suna dauke da cutar yanar ido da kuma glaucoma, wadanda ke bukatar tiyata.

Wani daga cikin wadanda suka amfana, Malam Yusufa Usman, ya bayyana cewa ya shafe sama da shekaru biyu yana fama da matsalar gani amma rashin kudi ya hana shi samun damar yin tiyata.

Ya ce tsawon wannan lokaci bai rika gani da kyau ba, amma a yanzu an yi masa tiyata kuma yana da kwarin gwiwar cewa ganinsa zai dawo yadda ya kamata.

Wata mata ma da ta amfana, Aisha Muntari, ita ma ta bayyana cewa ta kusa fidda rai kafin jin labarin wannan taimako, inda ta nuna yakinin cewa ganinta zai inganta nan ba da jimawa ba.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here