Mutane uku sun mutu a wani rikici tsakanin dillalan miyagun ƙwayoyi da jami’an tsaro a Katsina

Untitled 1 1824 (1)

Aƙalla mutane uku sun rasa rayukansu a ranar Asabar sakamakon wani rikici mai tsanani da ya ɓarke tsakanin jami’an tsaro da wasu da ake zargi dillalan miyagun ƙwayoyi ne a unguwar Koraman Nayalle da ke Sabuwar Unguwa a cikin birnin Katsina.

Rikicin ya fara ne a lokacin da jami’an tsaro suka yi yunkurin kama wani dillalin miyagun ƙwayoyi mai suna Uzairu, wanda aka fi sani da Kuda, inda suka ƙwace wayarsa ta hannu tare da wasu miyagun ƙwayoyi da ake zargin haramtattu ne.

Bayan haka, Kuda ya tara abokansa domin karɓo wayarsa daga hannun jami’an tsaron, lamarin da ya rikide zuwa tarzoma, inda aka harbe shi, daga bisani kuma aka tabbatar da mutuwarsa.

Wannan lamari ya haddasa fushin al’umma da tashin hankali a yankin, lamarin da ya ƙara tsananta rikicin har ya kai ga mutuwar mutane uku gaba ɗaya.

A yayin rikicin, an banka wa wani ofishin Hukumar Tsaro NSCDC, tare da ƙona wasu babura da ke yankin.

A lokacin da ake tattara wannan rahoto, yankin na cikin fargaba yayin da mazauna yankin ke tsoron sake ɓarkewar rikici, inda hukumomi ke ci gaba da ɗaukar matakai domin dawo da doka da oda.

Mai magana da yawun Hukumar Tsaro NSCDC ta Ƙasa Buhari Hamisu ya bayyana cewa an shawo kan lamarin, inda ya ƙara da cewa abokan mamacin sun yi yunƙurin lalata wasu ofisoshin hukumar da na ’yan sanda a yankin Filin Kanada, amma jami’an tsaro sun hana faruwar hakan, kuma tuni an fara bincike don gano Musa banin faruwar lamarin.

Shi ma mai magana da yawun yan sandan jihar DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa rikicin ya ƙara tsananta ne a lokacin jana’izar mamacin a ranar Lahadi.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here