Hukumar NSIB ta fara bincike kan jirgin Flybird da ya yi hatsari yayin sauka a filin jirgin sama na Kano

Flybird Jet Crash Lands 750x430

Hukumar kula da binciken tsaro da ta Najeriya ta fara gudanar da bincike kan hatsarin jirgin Hawker 800XP da rajista 5N-ISB da ya fuskanci matsala yayin sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a jihar Kano.

Jirgin, wanda kamfanin kula da jirage na Flybird ke gudanarwa, ya taso daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja zuwa Kano kafin faruwar lamarin a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an samu hatsarin saukar jirgin mai zaman kansa da kamfanin Flybird a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.

Majiyoyi masu tushe sun shaida wa jaridar Solacebase cewa jirgin na dauke da mutane 11, ciki har da ma’aikata uku da fasinjoji takwas.

Labari mai alaƙa: Da ɗumi-ɗumi :Jirgin sama ya yi hatsari a filin jirgin saman Kano

Daraktar hulda da jama’a da taimakon iyalai ta hukumar NBIS ta bayyana cewa yayin saukar jirgin, gaban tayar saukar jirgin ya rushe, amma dukkan mutanen da ke cikin jirgin sun sauka lafiya ba tare da samun rauni ba.

Hukumar ta kara da cewa bayan samun rahoton lamarin, ta tura tawagar bincike ta musamman, inda masu bincike za su duba tsarin jirgin, hanyoyin aiki, tarihin gyare-gyare da matakan da ma’aikatan jirgin suka dauka domin gano dalilan da suka haddasa faruwar lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here