2023: Wata ‘yar gwagwarmayar siyasa tana so Jamilu Ishaku ya zama gwamnan jihar Gombe

C2A23B62 4516 4DB5 B41E E5C8A72E3F18
C2A23B62 4516 4DB5 B41E E5C8A72E3F18

Wata ‘yar  gwagwarmayar siyasa kuma mai fafutuka dake zaune a Abuja, Liatu Danladi ta nemi  hamshakin dan kasuwa, Alhaji Jamilu Ishaku Gwamna da ya fito takarar gwamnan jihar Gombe.

Liatu wacce ita ce shugabar mata ta Sarduana Development Awareness (SDA), ta bayyana hakan a wata hira da ta yi  a Abuja, inda ta yi nuni da cewa ana kokarin ganin Ishaku ya zama gwamnan jihar Gombe a shekarar 2023.

A cewar ta, Ishaku yana tallafawa al’umma ta bangarori da dama musamman wajen samar da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar.

Ta ce, “Muna ganin yadda  Alhaji Jamilu Ishaku Gwamna yake tallafawa rayuwar al’ummar jihar Gombe a matsayinsa na dan kasa, zai fi kyau ya yi hakan a  matsayinsa na gwamnan jihar.”

Liatu Danladi ta yi nuni da cewa ya kasance mai taimakon al’ummar jihar Gombe yana da zuciyar taimako domin kuwa  ya bayar da gudunmuwa ba kadan ba wajen ci gaban jihar.

Ta kuma ba da tabbacin cewa mata da matasa za su yi duk mai yiwuwa wajen gudanar da yakin neman zabensa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here