Gwamnatin Kwara za ta kashe Naira biliyan 1.4 wajen sayen motocin alfarma ga ’yan majalisa duk da kalubalen tsaron da ke ƙara ta’azzara

gun gun 750x430

A yayin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a Jihar Kwara da ke Arewa ta tsakiya, binciken takardun kasafin kuɗin shekarar 2025 ya nuna cewa an ware kuɗaɗe har Naira biliyan 1.4 don sayen motocin alfarma ga mambobin majalisar dokoki ta jiha da kuma hukumar majalisar.

Bayanan kasafin kuɗin sun nuna cewa Naira miliyan 867.5 za a kashe wajen sayen motocin ’yan majalisa da manyan jami’an majalisar.

Haka kuma an ware Naira miliyan 569 domin sayen motocin Toyota Prado guda biyu ga shugabannin majalisa, Toyota Hiace guda biyu, da kuma Toyota Hilux guda ɗaya.

Jimillar kuɗin ya kai Naira biliyan 1.436 kacal a shekarar 2025, abin da ya tayar da muhawara kan fifikon kashe kuɗaɗen gwamnati, musamman ganin cewa matsalar tsaro na ci gaba da addabar al’umma a yankuna da dama na jihar.

A cikin wannan kasafin kuɗin, an ware Naira miliyan 350 ne kawai a matsayin kuɗin tsaro, sannan sayen kayan aikin tsaro ya samu Naira miliyan 37 kacal.

Al’umma da shugabannin ƙauyuka sun daɗe suna kira ga gwamnati da ta zuba jari sosai a tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.

Lamarin ya tsananta har ya sa hukumar NYSC ta sauya wurin gudanar da sansanin horaswa daga Yikpata a karamar hukumar Edu zuwa kwalejin Kwara da ke Ilorin, bayan damuwar da aka nuna kan tsaron matasa masu yiwa ƙasa hidima.

A ranar 13 ga Satumba 2025, daruruwan matasa daga wasu yankuna a Kwara ta Kudu sun fito zanga-zangar nuna adawa da garkuwa da mutane, inda suka rufe babban titin Ilorin–Omu-Aran–Kabba.

Sun yi gangami da kwalaye masu rubuce-rubuce irin su: “Mun gaji da biyan kudin fansa” da kuma “Isasshen tsaro muna nema, ba asara ba.” Wannan ya jawo hankalin ƙasa kan yadda ’yan bindiga ke addabar yankunan karkara.

Sai dai a gefe guda, kasafin kuɗin jihar ya nuna cewa an ware Naira biliyan 10 don gyaran otal otal ɗin Kwara, da kuma sama da Naira biliyan 1.3 don alawus, taruka da kayan jin daɗi.

A majalisar dokoki, Naira miliyan 665 an ware su don gina babban ɗakin taro mai kujeru 500.

Masu sukar lamirin gwamnati na ganin irin waɗannan kudaden alatu na nuna fifikon jin daɗin shugabanni fiye da tsaron al’umma.

Sun yi gargaɗi cewa idan ba a sake fasalin fifikon kasafin kuɗi ba, hakan zai ƙara jawo rashin amincewa da gwamnati, ya haddasa ƙarin zanga-zanga, tare da tsananta matsalar tsaro da ake fuskanta a halin yanzu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here