Malamai sun halarci gasar karatun Al-Qur’ani ta Shetty a Kano yayin da waɗanda suka yi nasara suka samu kyautar kuɗi

WhatsApp Image 2025 09 13 at 17.44.39 750x430

Gasar karatun Al-Kur’ani ta farko da Dr. Maryam Ibrahim Shettima (Dr. Maryam Shetty) ta shirya ta gudana a Kano, inda matasa daga sassa daban-daban na Najeriya suka nuna basirarsu ta hanyar kafafen sada zumunta.

Gasar mai taken “ReciteWithShetty” da jigon “Al-Kur’ani: Jagora wajen Tsarkake Sada Zumunta” ta yi nufin inganta ɗabi’a a yanar gizo da kuma ƙarfafa matasa su yi amfani da kafafen sadarwa ta fuskar alheri.

A cewar Dr. Shetty, wannan shiri ya haɗa Musulmi a ƙarƙashin karatun Al-Kur’ani tare da neman kawar da barna da rashin ɗa’a a shafukan sada zumunta.

Ta ce gasar ta kuma bai wa muryoyin masu fasaha damar bayyana, musamman waɗanda ba su da wata kafa ta shahara.

An gudanar da gasar ne ta dandalin TikTok, inda aka samu kusan mabiya dubu 15 a cikin ƙasa da makonni biyu, tare da bidiyoyi da suka kai sama da miliyan ɗaya.

Fitattun malamai irin su Sheikh Ibrahim Khalil da Sheikh Aminu Daurawa da kuma manyan baki ciki har da Hajiya Mariya Sanusi Dantata sun halarci taron.

A ƙarshe, Nuraddeen Mu’azu daga Abuja ya lashe gasar da maki 98.6, inda ya samu kyautar Naira miliyan 1.

Na biyu shi ne Muhammad Khaleed Idriss daga Bauchi da ya samu Naira 500,000, sannan Aisha Tahir Ibrahim daga Jigawa ta zo ta uku da Naira 250,000.

Dukansu kuma sun samu ƙarin Naira dubu 50,000 daga Kwamishinan Muhalli na Kano, Dr. Dahir Muhammad Hashim.

Sheikh Aminu Daurawa ta bakin wakilinsa ya yaba da ƙoƙarin Dr. Shetty tare da kiran ta da ta ci gaba da shirin, domin irin wannan gasa na iya gyara tunanin matasa da alaƙarsu da al’umma.

Aisha Tahir Ibrahim ta yi jawabi a madadin ’yan takara, inda ta bayyana godiya da cewa gasar ta zama babban ƙarfafawa ga matasa wajen rungumar Al-Kur’ani.

Taron ya jawo mahalarta da dama ciki har da malamai, ’yan siyasa da shugabannin al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here