Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya amince da nadin Malandi Umar Kura a matsayin babban sakataren a wata ma’aikata a jihar.
Solacebase ta ruwaito cewa kafin wannan nadin, Malandi ya rike mukamin Daraktan tsarin bayanan kasa a ofishin kula da filaye na jihar Kano.
Haka zalika Gwamna Ganduje ya amince da nadin Malam Isma’il Musa, a matsayin babban mai binciken kudi na jiha.
Wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na fadar gwamnatin Kano Ameen K. Yassar ya fitar a ranar Litinin, ta ce har zuwa hawansa wannan mukamin, Malam Isma’il shi ne Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar.
Sanarwar ta ce ya gaji Hajiya Amina Inuwa Sa’id, wadda ta yi ritaya daga aiki kwanan nan.
A cewar sanarwar, nadin nasu ya biyo bayan kwarewa da suke nunawa da kuma kishin kasa, wanda suke daga cikin manufofin aiki domin inganta jihar.
“Nauyi da ƙalubalen da suka rataya a wuyanku suna da yawa, amma ina da tabbacin za ku yi ƙoƙari don tabbatar da amanar matsayi mai daraja, ta hanyar azama, jajircewa da cikakken aiwatar da abubuwan da kuka samu kan aikin shekaru”, shugaban ma’aikatan ta jaddada, a cikin sanarwar.
‘’Gwamna Ganduje ya taya su murnar ci gaba da gudanar da ayyukansu tare da yi musu addu’ar Allah ya basu ikon gudanar da ayyukansu.
”Za a rantsar da sabbin wadanda aka nada nan gaba kadan”.












































