Yan Bindiga sun sace mai daƙin shugaban jam’iyyar APC da Ƴarsa a jihar Kwara

Gunmen new 750x430

Wasu mutane biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sace matar shugaban sam’iyyar All Progressives Congress (APC) na karamar hukumar Patigi a jihar Kwara, Alhaji Muhammad Swasun, tare da ‘yarsa.

An gano cewa wadanda aka sace su ne Hajiya Fatima, matar shugaban jam’iyyar, da kuma ‘yar sa mai suna Amina.

Lamarin ya faru ne a daren Lahadi a unguwar Sakpefu, lokacin da maharan suka tsallaka katangar gidan shugaban jam’iyyar suka shiga harabar gidan, inda suka rika harbe-harbe domin tsoratar da mazauna yankin.

Bayan haka ne suka kutsa ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, inda suka tarar da matar da ‘yar shugaban jam’iyyar, suka kuma yi awon gaba da su da bindiga.

Karin Labari: Gwamnatin Katsina ta tabbatar da kashe mutane 7 a harin ƴan bindiga

Wani jigon jam’iyyar a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin da safiyar Litinin, yana mai cewa shugaban jam’iyyar ya tsallake rijiya da baya saboda bai fada hannun maharan ba.

Shaidu sun ce maharan sun yi ta harbe-harbe na tsawon lokaci kafin su tafi da wadanda suka sace zuwa inda ba a sani ba.

A baya-bayan nan dai, yankin Patigi da wasu sassan Arewa ta Kwara sun sha fama da matsalar garkuwa da mutane, abin da ya sa jama’a ke ta kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su dauki matakai don kawo karshen lamarin.

Da aka tuntubi Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kwara, Adekimi Ojo, kan wannan batu, ya ce bai samu rahoton lamarin ba tukuna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here