Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta kama wani mutumi mai suna Mohammed Ali Abubakar dan kimanin shekara 55 bisa zargin safarar miyagun kwayoyi a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano (MAKIA).
Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa an kama Abubakar ne tare da wasu mutum biyar daga cikin mambobinsa da ke aiki a filin saukar jirgin.
Wannan ya biyo bayan binciken da ya gano cewa mutanen sun shirya jigilar miyagun ƙwayoyi zuwa kasa mai tsarki, wanda hakan yayi sanadiyar tsare wasu ‘yan Najeriya uku da suka je Umrah a gidan yari bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Hukumar ta bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, inda Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na hukumar, Femi Babafemi, ya jagoranta tare da Dr. Abdul Ibrahim, Daraktan Binciken Kudi da Kadarori, da kuma Theresa Asuquo, Daraktar Shari’a da Gurfanarwa.
NDLEA ta bayyana cewa lamarin ya biyo bayan koke-koken da iyalan wadanda aka kama – Maryam Hussain Abdullahi, Abdullahi Bahijja Aminu, da Abdulhamid Saddiq – suka shigar.
An zarge su da safarar miyagun ƙwayoyi bayan an haɗa sunayensu da wasu jakunkuna guda shida da ba nasu ba, ciki har da uku da aka gano suna ɗauke da miyagun ƙwayoyi.
Binciken NDLEA ya gano cewa jakunkunan na da alaka da ƙungiyar da Abubakar ke jagoranta, wanda ya tura su cikin jirgin Ethiopian Airline mai lamba ET940 ranar 6 ga Agusta, 2025, jirgin da waɗannan matafiyan uku suka hau daga Kano zuwa Jeddah ta Addis-Ababa.
Wasu ma’aikatan Skyway Aviation Handling Company, waɗanda suke cikin ƙungiyar, sun yi amfani da sunayen waɗannan matafiya ba tare da saninsu ba wajen ɗora jakunkunan.
Yanzu haka mutane shidan da aka kama daga cikin ƙungiyar na hannun hukumar ta NDLEA, inda tuni huɗu daga cikinsu aka riga aka kai su kotu.
Sun bayar da bayanai na gaskiya kan yadda aka shirya lamarin, ciki har da amincewa da karɓar kuɗi N200,000 domin ɗora jakunkuna.
NDLEA ta bayyana cewa ta fara tattaunawa da Hukumar General Directorate of Narcotics Control (GDNC) ta Saudiyya don ganin an saki waɗannan ‘yan Najeriya da ba su da laifi.
Haka kuma, Shugaban hukumar, Janar Marwa (Rtd), zai gana da hukumomin Saudiyya a yayin wani taron kasa da kasa kan miyagun ƙwayoyi domin gabatar da hujjojin bincike.
Hukumar ta tabbatar da cewa tana da cikakken ƙuduri na yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, amma ba za ta lamunci a hukunta waɗanda ba su da laifi ba.









































