Gwamnatin Jihar Kano ta sake bude masana’antar sarrafa taki ta Dorayi a wani mataki na karfafa shirin ta na “Waste-to-Wealth,” wato sauya shara zuwa arziki, da nufin kyautata yadda ake sarrafa shara, bunkasa noma na gargajiya da kuma samar da damammakin aikin yi.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahir M. Hashim, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa a ranar Talata.
Dr. Hashim ya ce sake bude wannan masana’anta da goyon bayan Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kasance babbar nasara wajen tabbatar da muhalli mai tsafta da lafiya a fadin jihar.
A cewar sa, masana’antar za ta rika sauya sharar gida zuwa taki na gargajiya wanda zai taimaka wajen kara ingancin kasar noma da lafiyar jama’a, tare da taimakawa wajen kare halittu masu rai da ke cikin muhalli.
Ya kuma jaddada cewa takin da ake samarwa a masana’antar yana da cikakken sinadarai na gargajiya ne, wanda baya cutar da rayuwar dabbobin ruwa idan ruwa ya wanke shi ya shiga magudanan ruwa.
Kwamishinan ya kuma bukaci hadin gwiwar masu ruwa da tsaki da abokan hulda wajen fadada wannan shiri da kuma habaka dorewar muhalli a fadin jihar.












































