Buhari ya isa jihar Ogun domin kaddamar da ayyuka

FB IMG 1642078700981
FB IMG 1642078700981

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Ogun domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Prince Dapo Abiodun ya aiwatar.

Abiodun da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar ne suka tarbe shi da misalin karfe 10.40 na safe a unguwar Mojoda da ke Ijebu-Ode, inda aka shirya bikin kaddamar da babbar hanyar Ijebu-Ode-Mojoda-Epe mai nisan kilomita 14.

Haka kuma ana sa ran Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka da suka hada da filin ajiye motoci na Gateway City Gate Monument Park da tashar Motar Sagamu.

Sauran ayyukan sun hada da: rukunin gidaje guda biyu wanda ko wanne ke dauke da gidaje 527 a Kobape a karamar hukumar Obafemi-Owode da kuma rukunin gidaje 83 da ke Kings Court Estate, Oke-Mosan a Abeokuta.

Buhari ya kuma shirya yin taron masu ruwa da tsaki a masaukin shugaban kasa dake Abeokuta domin kawo karshen ziyarar.

A halin da ake ciki kuma, birnin Abeokuta na sanye da wani sabon salo inda aka kawata manyan tituna, gadoji da sauran manyan cibiyoyi da wuraren jama’a da kyau a wani bangare na shirye-shiryen kara launi a cikin shirin.

Hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC da hukumar sa ido da kula da ababen hawa na jihar sun rufe wasu manyan titunan da ba a iya zirga-zirga.

Sai dai an samar da wasu hanyoyin da aka bude wa masu ababen hawa a jihar yayin da ziyarar ta kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here