Shekaru bakwai bayan tserewa daga gidan yari bayan samunsa da laifin safarar miyagun kwayoyi, jami’an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa sun kama wani shahararren mai rarraba haramtattun kayayyaki a babban birnin tarayya Abuja, Ibrahim Momoh, wanda aka fi sani da Ibrahim Bendel. Hukumar, NDLEA
A cewar hukumar, an kama wanda ake zargin ne a wani samame da suka kai maboyarsa da ke Filin Dabo, a yankin Dei-Dei a babban birnin tarayya Abuja.
SOLACEBASE ta rahoto cewa an fara kama Ibrahim Momoh ne a ranar 27 ga Nuwamba 2014 da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 385.1, an gurfanar da shi a gaban kuliya, aka yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai da rabi a gidan yari a ranar 22 ga Yuli 2015 amma a lokacin da yake zaman gidan yari a Kuje, ya tsere daga gidan yari. ranar 16 ga Mayu, 2016.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Femi Babafemi, Daraktan NDLEA, Media & Advocacy, Abuja, ya fitar a ranar Lahadi.











































