A yau ne Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, za ta yanke hukunci kan ƙarar da gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya shigar gabanta, inda yake kalubalantar soke zaɓen da ya ba shi nasara da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta yi a baya.
Adeleke da jam’iyyarsa ta PDP sun buƙaci kotun ɗaukaka ƙaran da ya jinge hukuncin kotun baya da ya soke nasararsa.
A ranar 27 ga watan Janairu ne, Mai shari’a Tetsea Kume, na kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe a lokacin yanke hukunci, ya ce Hukumar zaɓe ta INEC ba ta bi tanade-tanaden dokar zaɓe da na kundin tsarin mulki yadda ya kamata ba.
A cewar kotun, Idan aka cire ƙuri’un da ake zargin an yi aringizo, Adegboyega Oyetola na APC ya samu yawan ƙuri’u 314,921 yayin da Ademola Adeleke na PDP ya samu ƙuri’u 290,266.










































