Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni 5

Buhari signs sabo 1
Buhari signs sabo 1

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinoni kasa 5 a Hukumar Tsara Alashi ta Kasa (RMAFC), kwana biyar kafin ya sauka daga mulki

Buhari ya ba su rantsuwar aiki ne gabanin fara taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ta karshe a gwamnatinsa a ranar Laraba, a Fadar Shugaban Kasa.

Sabbin Kwamishinonin da aka rantsar su ne: Hawa Aliyu daga Jihar Jigawa da  Rekiya Haruna (Kebbi) da Ismaila Agaka (Kwara) da Sanata Ayogu Eze (Enugu) da kuma Peter Opara (Imo).

Sauran su ne Kolawole Abimbola daga Jihar Oyo, sai kuma Ayuba Ngako daga Yankin Babban Birnin Tarayya.

A yayin zaman, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya mika rahoton kwamitin da ya jagoranta kan inganta bangaren lafiya, domin samar da jadawali da nagartaccen tsarin kula da lafiya ga daukacin ’yan kasa cikin sauki.

Daga cikin shawarwarin kwamitin akwai batun kara kudaden da ake ba wa bangaren daga kashi 10 cikin 100.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here