Ƴar wasan gaba ta Super Falcons, Ifeoma Onumonu, ta sanar da yin ritaya daga kwallon kafa bayan fiye da shekaru 10 tana taka leda a Amurka, Faransa da Najeriya.
Onumonu ta bayyana hakan ne a wani rubutu mai cike da godiya da ta wallafa a shafin Instagram a ranar Asabar, inda ta ce wannan mataki shi ne ƙarshen tafiya ta dabi’a da ta fara tun tana da shekara takwas da haihuwa.
Tsohuwar ƴar wasan ta tuna yadda ta fara wasa a ƙungiyar yara mai suna Magic a Amurka, tana buga ƙwallo ba tare da tsari ba sai dai kawai sha’awar gudu da cin ƙwallo.
Ta ce burinta ba wai yafi so da sha’awar buga wasa ba, ba wai cin nasara ko rashin nasara ba.
Mai shekara 31 a duniya ta bayyana cewa sha’awarta ga wasan ƙwallo ta yi jagora gare ta na tsawon shekaru 22, inda ta samu damar lashe kofin NWSL Championship, a wakiltar Najeriya a Gasar Olympics da Gasar Cin Kofin Duniya, tare da taimaka wa Super Falcons wajen ɗaga kofin nahiyar Afrika a karo na 10.
Ƴar asalin Amurka wadda ta fara bugawa Super Falcons wasa a 2021, ta shiga jerin ƴan wasan Najeriya a Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata a 2023 da kuma Gasar Olympics ta Paris a 2024.
Haka kuma, ta buga wasa a Gasar Cin Kofin Afrika ta Mata a Maroko a 2025, inda Super Falcons suka kafa tarihin lashe kofin karo na 10, ko da yake ita dai ta taka leda na tsawon minti 54 kacal a wasan da suka tashi 0-0 da Aljeriya.
A matakin kungiy, Onumonu ta fara ne da Boston Breakers a gasar National Women’s Soccer League, sannan ta wakilci Portland Thorns, Reign FC, Utah Royals da NJ/NY Gotham FC kafin ta tafi Faransa ta buga wasa da Montpellier HSC.
Ta kuma fito daga shirye-shiryen kwallon kwalejin California Golden Bears, inda ta fara wakiltar Amurka a matakin ƴan kasa da shekaru 23 kafin ta sauya sheka zuwa Najeriya.
Yar wasan ta bayyana cewa ritayarta ba ta nufin rabuwar ta da kwallon kafa gaba ɗaya ba, illa dai sabon mataki ne a rayuwarta.
Onumonu ta yi godiya ga kowa da kowa da ya mara mata baya a tafiyarta, ciki har da malamai, ƙungiyoyi, abokan wasa, likitoci, masoya da iyalinta.
Ta ƙara da cewa ko da yake lokacin ta na buga wasa ya ƙare, kaunarta da sadaukarwarta ga wasan kwallon kafa ba za su gushe ba.













































