Kungiyar Cigaban Arewa ta ACF, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara wa’adin dena karɓar tsofaffin takardun naira.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na kungiyar Arewa Consultative Forum, ACF, reshen jihar Kano, Bello Galadanci ya fitar a yau Asabar.
Sanarwar ta ce wa’adin ranar 31 ga watan Janairu da gwamnatin tarayya ta kayyade ya kusan dakile ayyukan zamantakewa da tattalin arziki a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa kin karbar tsoffin takardun naira a hada-hadar kasuwanci saboda fargabar cikar wa’adin saka kudaden a bankunan kasuwanci janyo wa talaka wahala.
“Hakan ya kara wa talakawa wahala a halin yanzu, domin har yau bankuna suna baiwa kwastomomin tsofaffin takardun Naira da wa’adin kwanaki kadan ya rage.
“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba matakin da ta dauka ta hanyar tsawaita wa’adin ranar 31 ga watan Junairu na cikar tsofaffin takardun kudi na Naira domin baiwa mazauna yankin damar musanya tsohuwar naira da sabbin takardun Naira,” in ji sanarwar.













































