Ƙudirin haraji ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai

HOUSE OF REPS MEMBERS 720x430 (1)

Majalisar wakilan ta amince da ƙudirin haraji a karatu na biyu, bayan zazzafar muhawara kan ƙudirin tsakanin ‘yan majalisar.

Tun da farko majalisar ta haɗe duka ƙudurorin harajin huɗu da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike mata a shekarar da ta gabata zuwa ƙuduri guda kafin fara muhawara a kansa.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne ya jagoranci muhawarar, wanda ya ce kuɗurin zai taimaka wajen farfaɗo da fannin karɓar haraji na ƙasar nan.

Farfesa Ihonvbere ya yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar gwamnonin bisa kwaskwarimar da suka yi wa ƙudurin, da nufin magance matsalolin da aka yi fargabarsu tun da farko.

Labari mai alaƙa: Gwamnatin Kano ta yi watsi da kudirin gyaran haraji

Ƙudirin harajin ya haifar da zazzafar muhawara takanin ‘yan ƙasar nan, musamman waɗanda suka fito daga yankin arewa, inda suka riƙa zargin cewa sabon ƙudirin zai cutar da yankin.

A farkon wannan shekarar ne ƙungiyar gwamnonin ta ƙasa suka amince da kuɗurin, bayan sun yi masa kwaskwarima dangane da yadda za a raba harajin VAT.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here