Zargin Zamba: Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon Ministan Wutar Lantarki

EFCC EFCC Sabo

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa ta sake gurfanar da tsohon ministan wutar lantarki da ƙarafa, Dokta Olu Agunloye, bisa zargin aikata laifuka cikin har da yarjejeniyar gina tashar samar da wutar lantarki ta Mambila.

An gurfanar da shi a gaban mai shari’a Jude Onwuegbuzie na babbar kotun babban birnin tarayya da ke Apo, Abuja, kan tuhuma bakwai da aka sake fasalta. Tuhumar ta haɗa da karya umarnin shugaban ƙasa, da yin jabun takardu da karɓar rashawa.

Lauyan masu shigar da ƙara, Malam M. K. Hussain, wanda ya wakilci babban lauya Abba Muhammed, ya shaida wa kotu cewa sun gabatar da ƙarin tuhuma.

Ya roƙi kotu ta bai wa wanda ake tuhuma damar amsa wannan sabuwar tuhuma. Lauyan Agunloye, Adeola Adedipe, bai yi ƙin amincewa da hakan ba, inda aka karanta masa tuhumar, sai dai ya ce shi ba shi da laifi.

Hukumar ta bayyana cewa a ranar 22 ga watan Mayu, shekara ta 2003, Agunloye ya karya umarnin shugaban ƙasa da aka bayar a taron majalisar zartarwa ranar 21 ga watan Mayu, 2003.

Daga nan kuma ya aika wasiƙar amincewar gwamnatin tarayya ga kamfanin Haske da Wutar Lantarki na Sunrise, don aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila mai ƙarfin megawatt dubu uku da dari tara da sittin.

Har ila yau, an zarge shi da haɗa baki da shugaban kamfanin, Leno Adesanya, wanda yanzu ya ɓoye, wajen jabun wasiƙar yarjejeniyar aikin.

Hukumar ta ƙara bayyana cewa a shekarar 2019, tsohon ministan ya karɓi kuɗaɗe daban-daban da suka kai naira miliyan biyar da dubu dari biyu da goma sha biyu daga kamfanin da kuma Adesanya, ta hanyar wani Jide Abiodun Sotirin, a cikin asusun bankinsa na Guaranty Trust Bank.

I’mAn ce waɗannan kuɗaɗen sun shafi amincewar gwamnatin tarayya ga aikin tashar wutar lantarki ta Mambila.

Sai dai Agunloye ya dage cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa ba, inda ya bayyana cewa shi mai gaskiya ne a cikin al’amuran da suka shafi aikin Mambila.

Bayan amsa tuhumar, mai shari’a Onwuegbuzie ya dage sauraron ƙarar zuwa ranar 9 ga watan Oktoba domin ci gaba da gurfanar da shaidun hukumar. Wannan na zuwa ne bayan lauyan gwamnati ya nemi a soke ranakun 22 da 25 ga watan Satumba da aka tsara tun farko.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here