Zamfara Ta Hana Haƙar Ma’adanai Ba bisa Ka’ida ba

Mining
Mining

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya hana gudanar da ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, ya kuma umarci jami’an tsaro da su dauki tsattsauran mataki kan masu karya doka.

Tsawon shekaru, hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar Zamfara ya kara ruruta wutar ‘yan fashi da sauran miyagun ayyuka.

Gwamna Lawal, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan barna da kuma aiwatar da matakan kare lafiya da jin dadin jama’a.

Sanarwar ta ce, an baiwa jami’an tsaro umarni da su dauki kwakkwaran mataki tare da harbe duk wanda aka samu yana aikin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here