Yanzu-yanzu: Fubara ya ba da umarnin sake zaɓen ƙananan hukumomi bayan hukuncin kotun ƙoli

Siminalayi Fubara 1

Gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Rivers (RSIEC) za ta sake gudanar da sabon zaben kananan hukumomi bayan da kotun koli ta yanke hukunci kan rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar.

Ya kuma umurci shugabannin kananan hukumomi masu barin gado da su mika ragamar mulki ga shugabannin kananan hukumomin a ranar Litinin 3 ga Maris 2025.

Karanta: Kotun koli ta kori karar da Fubara ya shigar yana kalubalantar Amaewhule a matsayin shugaban majalisa

Fubara, wanda ya bayyana hakan a yammacin Lahadi a gidan gwamnati da ke Fatakwal, yayin da yake mayar da martani ga hukuncin da kotun koli ta yanke, ya bayyana cewa matakin ya zama tilas ne sakamakon haramcin tsarin riko a kananan hukumomi na Najeriya.

Ya ce duk da cewa gwamnatinsa ba ta amince da hukuncin ba, amma ya zama dole ta bi umarnin da kotu ta bayar a matsayin gwamnati mai bin doka da oda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here