Tinubu ya bada umarnin karɓo bashin Naira biliyan 30 da ake bin dillalan kayan noma

Tinubu Tinubu sign 750x430

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci Bankin Noma (BOA) da ya biya bashin da ake bin dillalan kayan noma da masu samar da kayayyakin noma a ƙarƙashin Shirin Ƙara Bunƙasar Noma da Agro-Pocket (NAGS-AP), bayan sakin Naira biliyan 30 daga Bankin Raya Afirka (AfDB).

Wannan mataki, wanda aka ce zai hanzarta tallafa wa manoma tare da tabbatar da kwanciyar hankali wajen samar da abinci a Najeriya, ya kuma naɗa BOA a matsayin mai kula da dukkan kuɗaɗen shirye-shiryen tallafin noma.

A wata sanarwa da Judith Ekwebelem, shugabar hulɗa da waje ta BOA, ta fitar, an bayyana cewa wannan mataki zai zama sabon babi a harkar noma.

An umarci bankin da ya tabbatar da biyan kuɗaɗe cikin gaggawa ta amfani da tsarin e-wallet, inda ya yi alkawarin kammala biyan duk masu bin bashin da suka cancanta cikin awa 24, tare da bayar da rahoton ci gaban biyan kuɗi duk mako har sai an kammala.

BOA ya bayyana cewa wannan Naira biliyan 30 ita ce kaso na biyu da Bankin Raya Afirka ya fitar domin aiwatar da shirin NAGS-AP, wanda aka nufa da shi ne wajen biyan hakkokin dillalan kayan noma da suka halarci shirin damina da na rani na shekarar 2024.

A cewar Ekwebelem, Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, ya umurci a baiwa lamarin muhimmancin gaggawa.

Shugaban BOA, Ayo Sotinrin, ya bayyana cewa an kaddamar da biyan kuɗaɗen a hukumance tun ranar 18 ga Satumba 2025 tare da ofishin NAGS-AP, inda aka mika jerin sunayen waɗanda za su ci gajiyar shirin.

Ya ce wannan ba wai biyan kuɗi ne kawai ba, illa dai wata alamar sadaukarwa ce wajen tabbatar da tsaron abinci da kuma bunƙasa noma daga matakin rayuwar yau da kullum zuwa kasuwanci mai ɗorewa da riba.

Ya kara da cewa BOA ta kafa sharudda na musamman ga dillalan kayan noma da masu kaya da za su ci gajiyar biyan, ciki har da buɗe asusun BOA, kasancewa cikin jerin waɗanda aka amince da su a shirin kafin shekarar 2025, da kuma tabbatar da sun taba karɓar wani biyan a baya.

Ana sa ran kammala biyan cikin rana ɗaya da zarar an tabbatar da bayanan.

Sotinrin ya bukaci duk masu cin gajiyar shirin da su gaggauta cika waɗannan sharuɗɗan, yana mai gargadi cewa jinkiri wajen bin umarni na iya kawo tsaiko wajen samun kuɗaɗen.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here