Sojojin Najeriya sun musanta wani rahoton da aka bayyana a internet da ke cewa ‘yan bindiga sun mamaye sansanin sojoji tare da sace manyan bindigogi guda shida da harsasai sama da 30,000 a Obanla, Jihar Kwara.
Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar Sojojin ƙasa, sashen runduna ta 2, Laftanar Kanal Polycarp Okoye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Ibadan ranar Lahadi.
Ya ce akasin abin da aka wallafa, dakarun Bataliya ta 148 (Rear) suna ci gaba da gudanar da aikin share fage a jihohin Kogi da Kwara, inda suke samun gagarumin nasara wajen yakar masu laifi.
Okoye ya bayyana cewa dakarun sun kafa matsayi mai ƙarfi a yankin kan iyakar Kwara da Ekiti, inda suka kashe ‘yan bindiga biyu tare da kwato sabbin bindigogi biyu kirar AK-47 a wata musayar wuta da suka yi da su kwanan nan.
Ya ƙara da cewa babu wani lokaci da sansanin sojoji ya fadi ko kuma aka kwace makamai ko harsasai daga hannunsu kamar yadda rahoton ya yi ikirari.
Ya ce labarin ƙirƙira ne da aka yi don yaudarar jama’a da kuma rage ƙarfin gwiwar dakarun da ke aiki tukuru don dawo da zaman lafiya a yankin.
Mai magana da yawun rundunar ya jaddada cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da murkushe dukkan nau’o’in laifuka a faɗin ƙasar nan, tare da tabbatar da cewa an rushe duk wata cibiyar ‘yan ta’adda a jihohin Kogi, Kwara da maƙwabtan su.
Ya kuma roki jama’a da su yi watsi da wannan rahoto na ƙarya tare da ci gaba da bai wa rundunar bayanai masu inganci da za su taimaka wajen nasarar ayyukan tsaro a ƙasar.
NAN












































