Sojoji Sun Kubutar Da Wasu Dalibai 4 Da Aka Sace A Jami’ar Tarayya Ta Gusau

nigerian army training (1)
nigerian army training (1)

Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation HADARIN DAJI tare da hadin gwiwar ‘yan sandan Najeriya a jihar Zamfara sun sake kubutar da wasu daliban jami’ar tarayya Gusau (FUGUS) guda 4 da wasu ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su da dare a ranar Asabar 14 ga watan Oktoba, 2023 daga gidan da suka yi garkuwa da su.

An gudanar da aikin ceton ne a kan lokaci kuma a cikin gaggawar amsa kiraye-kirayen da mazauna yankin suka yi, kamar yadda wata sanarwa da Kyaftin Yahaya Ibrahim, jami’in yada labarai na rundunar, Hadarin Daji, ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here