Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wasu ‘yan bindiga tare da kubutar da wasu mutane da su ka yi garkuwa da su a jihar Sokoto.
Wannan na kunshe ne cikin wani sako da rundunar sojin ta wallafafa a shafinta na X.
Ta ce dakarunta na Hadarin Daji sun kaddamar da wani atisaye a kauyen Bauni da dajin Bauni a jihar ranar 14 ga watan Disamba.
Rundunar ta kara da cewa dakarunta sun shafe sa’o’i masu yawa suna musayar wuta da ‘yan bindigar.
Karanta wannan:Yanzu-yanzu: tsohon gwamnan jihar Anambra ya rasu
Sanarwar ta ce bayan da sojojin suka matsa wa ‘yan bindigar sai suka tsere suka bar maboyarsu.
Lamarin da ya sa sojojin suka samu nasarar kubutar da mutum shida da suke garkuwa da su.

Makaman da aka gano sun hadar da bindiga kirar AK-47 biyu da kuttun adana alburusai 19, da alburusai.

Sai bindigogin toka biyu da Babura da na’urorin oba-oba da kuma sauran kayayyaki
Sanarwar ta ce sojojin sun lalata maboyar ‘yan bindigar tare da ababuwan da suka gano nan take.












































