Rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ta musanta rahotannin da ke cewa kungiyar IS ta yi garkuwa da wasu ‘yan sanda a makarantar horas da ‘yan sanda da ke limankara, karamar hukumar Gwoza ta jihar.
Mista Audu Umar, kwamishinan ‘yan sandan jihar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a Maiduguri.
Umar ya ce rahoton da ke ikirarin cewa an sace ‘yan sandan da ba a tantance adadinsu ba a makarantar, labarin karya ne.
Wasu rahotanni sun nuna cewa mayakan ISWAP sun yi awon gaba da wasu ‘yan sanda da ba a tantance adadinsu ba bayan wani hari a makarantar da misalin karfe 8:22 na safiyar ranar Alhamis.
Sai dai Umar ya ce babu wani dan sanda da aka sace a lokacin da lamarin ya faru, inda ya ce dukkan ‘yan sandan 13 da ke makarantar suna cikin koshin lafiya domin sun samu nasarar dakile harin na ‘yan ta’adda.
Ya bayyana cewa rundunar ba ta rasa ma’aikata ko makami ba a yayin harin.
Kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci ‘yan jarida da su yi iyakacin kokarinsu wajen tabbatar da rahotonsu kafin ciyar da jama’a.













































