Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana ci gaba da gudanar da samame a yankin da ke kusa da asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza.
A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce kawo yanzu ta kashe mutane casa’in a kusa da asibitin kuma ta binciki sama da mutane dari uku da take zargi.
Karin labari: Gwamnatin Tarayya ta bayyana Tukur Mamu da mutum 14 kan ta’addanci
Kafofin yada labaran Falasdinawa sun ce hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama sun kashe mutane da dama a cikin dare, ciki har da akalla mutane ashirin da uku da ke shirya matakan tsaro domin kai kayan agaji zuwa birnin Gaza.
Isra’ila dai ba ta ce uffan kan wannan zargi ba.