Rikicin Wike da jami’in sojin ruwa: Kayan Soji na wakiltar ikon Ƙasa -Irabor

WhatsApp Image 2025 11 13 at 12.55.02 750x430

Tsohon shugaban rundunar sojin ƙasar nan, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya bayyana cewa rashin girmama jami’an da ke sanye da kayan soja ko na tsaro, yana nufin raina ikon da ƙasa ke da shi baki ɗaya.

A wani jawabi da ya gabatar a taron tattaunawar ƙasa kan kafafen yaɗa labarai, ta’addanci da tsaron ƙasa, a taron ƙungiyar editocin Najeriya karo na 21 a birnin Abuja, Janar Irabor ya ce kayan da jami’an tsaro ke sanyawa ba wai don mutum ɗaya bane, suna wakiltar mutunci, iko da ikon mallakar ƙasa.

Ya bayyana cewa duk wanda ya zagi ko ya yi abin da bai dace ba ga jami’in tsaro, ko matashi ne ko babba, yana tozarta ikon ƙasa ne kai tsaye.

Ya kuma tunatar da jama’a cewa rundunar soja na aiki ne bisa ƙa’ida, kuma babu wanda yake da hurumin cin zarafin wanda ke ƙarƙashinsa.

Janar Irabor ya ce ko shi da yake janar, ba shi da ikon dukan sojansa, domin akwai hanyoyin hukunta laifi da aka tanadar, waɗanda ke tabbatar da cewa ƙasa tana bin doka.

Karin labari: Atiku ya musanta cewa ya bai wa jami’in sojan ruwa mota ƙirar SUV saboda rikicinsa da Wike

Ya ƙara da cewa ko da Ministan Babban Birnin Tarayya yana da ikon kula da harkokin ƙasa, dole ne a ci gaba da mutunta kayan da jami’an tsaro ke sanyawa, domin suna wakiltar ikon da tsarin doka ya gina.

Tsohon shugaban rundunar tsaron ƙasar ya nuna damuwa kan yadda ake rasa ilimin ɗabi’ar ɗan ƙasa da darasin girmama cibiyoyin gwamnati, yana mai cewa kafafen yaɗa labarai su kasance masu gina ƙasa ta hanyar rubuce-rubucen da ke karfafa girmama hukumomin tsaro da dokoki.

Ya kuma yi kira da a guji nuna raini ko tsokana ga jami’an da ke sanye da kayan aiki, yana mai jaddada cewa idan jami’in tsaro ya yi laifi, doka ce za ta hukunta shi, amma dole ne kayan da yake sanyawa su sami girmamawa domin su ne ginshiƙan tsari da zaman lafiya.

Janar Irabor ya gargadi ‘yan ƙasa da shugabanni da su guji yin abin da zai rage darajar alamomin ikon ƙasa, yana mai cewa idan aka ci gaba da haka, Najeriya za ta fada cikin halin dubu.

Ya kammala da kira da cewa dole ne a girmama kayan soja da abin da suke wakilta domin kiyaye tsarin ƙasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here