Maniyyaci ɗan Kano ya rasu a ƙasar Saudiyya

WhatsApp Image 2025 06 04 at 11.16.40

Wani maniyyaci dan jihar Kano, Malam Shu’aibu Jibrin, ya rasu a kasar Saudiyya sakamakon gajeriyar jinya a lokacin da yake aikin Hajjin bana.

SolaceBase ta ruwaito cewa Malam Shu’aibu Jibrin ya rasu ne jiya Talata a asibitin Sarki Abdulaziz.
Jikansa Sama’uddin Aliyu Kadawa, wanda shi ma ya na kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajji, ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da Solacebase.

A cewar Sama’uddin Aliyu, marigayi Shu’aibu Jibrin manomi ne daga garin Gargai da ke karamar hukumar Bebeji.

Ya bayyana cewa, duk da ya na da tarihin ciwon Ulcer da hawan jini, likitocin asibitin sun tabbatar da cewa ya kamu da ciwon bugun zuciya.

Sama’uddin Aliyu ya ci gaba da cewa, “Lafiya ya bar gida, bayan ya kamu da rashin lafiya an kwantar da shi a Asibitin Sarki Abdulazeez na tsawon kwanaki biyu kuma an sallame shi bayan samun saukin sai dai daga bisani ya rasu.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here