Tashi da saukar jirage ya samu tasgaru a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano MAKIA, sakamakon rikice da yake faruwa tsakanin gwamnatin tarayya da ma’aikatan hukamar da ke kula da zirarga zirgar jirgin sama ta kasa.
Jaridar solacebase ta rawaitu cewa jiragen da zasu tashi yau Litinin ba samu damar tashi ba sakamakon rikicikin.
Jirgin da basu samu damar tashi ba sun hada da AZMAN da kuma Max Air da ya kamata su tashi zuwa Abuja da Lagos.
Jaridar solacebase ta tattaro bayanan cewa manyan mutane da dama abin ya rutsa dasu, wadan da suka hada da ‘yan majalisu da mataimakan gwamnoni.













































