Kwara: Ana fargabar ƴan bindiga sun yi garkuwa da wace mai juna biyu da yara da wasu mutane a wani sabon hari da suka kai

Gunmen scaled 1 750x430

Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Isapa da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka yi garkuwa da mutane goma sha ɗaya daga cikin mazauna yankin, lamarin da ya jefa al’umma cikin matsanancin fargaba.

Ƴan bindigar fiye da ashirin sun mamaye ƙauyen ne tare da garken shanu a ranar Litinin, suna harbe-harbe ba kakkautawa.

Wata tsohuwa ta ji rauni bayan harsashi ya same ta wajen harbe-harben da suka tayar da hankula.

Wani jagoran al’umma ya bayyana cewa daga cikin mutanen da aka sace akwai bakwai daga gida guda ɗaya, ciki har da mace mai juna biyu, mata masu shayarwa biyu da ƙananan yara da dama.

Jerun sunayen waɗanda aka sace sun haɗa da Talatu Kabiru, Magaji mai shekaru shida, Kande mai shekaru biyar, Hadiza mai shekaru goma, Mariam mai shekaru shida, Saima mai shekaru biyar, Habibat matar aure, Fatima Yusufu wadda ke ɗauke da juna biyu, Sarah Sunday mai shekaru ashirin da biyu, Lami Fidelis mai shekaru ashirin da uku wadda ke shayarwa, da Haja Na Allah wadda ita ma mai shayarwa ce.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun ratsa unguwanni daban-daban na ƙauyen, suna harbin harsasai a bangon gidaje da ƙofofi.

An tarar da harsasan bindiga kirar AK-47 a warwatse bayan maharan sun tsere, yayin da rundunar ’yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa ba tukuna.

Harin ya zo ne bayan kimanin makonni biyu da maharan suka kai hari a cocin Christ Apostolic da ke Eruku, inda aka sace mutane talatin da takwas sannan wasu suka rasa rayukansu.

Duk da cewa daga baya an saki waɗanda aka yi garkuwa da su, lamarin ya ƙara tsananta fargaba a yankin.

 

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here