Babban kwamitin tsare-tsaren kuɗi na babban bankin ƙasa CBN ya sanar da cewa ƙimar kuɗin ruwa da za ta ci gaba da kasancewa a kan kashi 27 cikin ɗari.
Wannan bayanin ya fito daga gwamnan babban bankin ƙasa CBN Olayemi Cardoso, a wani taron manema labarai da aka yi yayin zama na 303 na kwamitin a Abuja.
Kwamitin ya kuma sake tabbatar da cewa an daidaita ajiyar kuɗaɗe na dole ga bankunan kasuwanci zuwa kashi 45 cikin ɗari, ga bankunan dillalai kashi 16 cikin ɗari, yayin da aka ƙayyade kashi 75 cikin ɗari ga kudaden gwamnati.
Haka zalika an tabbatar da rabon kudin ruwa a kan kashi 30 cikin ɗari tare da daidaita matsayin hanyoyin jinginar kuɗi zuwa +50 da -450 makin tushe a kan ƙimar kudin ruwa.
Kwamitin ya ce waɗannan matakan na nuna tsayuwar daka wajen ganin an ci gaba da rage hauhawar farashin kayayyaki, inda aka bayyana cewa an riga an fara ganin raguwar hauhawar sakamakon inganta harkokin kuɗi, zamanin musayar kuɗi da ya ɗan daidaita, da kuma tsayayyen farashin man fetur.
Haka kuma kwamitin ya yi nuni da cewa duk da wannan ci gaba, hauhawar farashin kayayyaki har yanzu yana kan matakin da ke buƙatar ƙarin matakai tare da haɗin gwiwar hukumomi domin sauke shi ƙasa.
Ya kuma ce an samu cigaba a yunkurin ƙarfafa jarin manyan bankuna, inda aka tabbatar da cewa bankuna 16 sun cika ka’idojin da ake buƙata.
A batun yanayin tattalin arziƙin duniya, Cardoso ya bayyana cewa ana sa ran samun farfaɗowa a matsakaicin lokaci, duk da cewa matsalolin kasuwanci tsakanin Amurka da wasu manyan abokan cinikayyar ta na iya kawo tangarda.
Kwamitin ya yi hasashen cewa hauhawar farashin kayayyaki a duniya zai ci gaba da kasancewa sama da matakin da ake da shi kafin annobar korona, yayin da babban bankin ya sake tabbatar da aniyar ci gaba da amfani da tsare-tsaren kuɗi bisa bincike domin tabbatar da zaman lafiyar farashi da ƙarfafa tsarin kuɗin ƙasa.













































