Kotu ta yi watsi da karar El-Rufai na hana ICPC rufe asusun bankinsa

Nasir el Rufai new 750x430

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar domin hana Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffukan da Suka Shafi Hakan (ICPC) da wasu hukumomi rufe asusun bankinsa ko ƙwace kadarorinsa.

Alƙalin kotun, mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta yi watsi da ƙarar a ranar Alhamis, bayan ta bayyana cewa shigar da ita ya saɓa wa tsarin amfani da kotu yadda ya kamata.

El-Rufai ya shigar da ƙarar ne a kan ICPC, Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, a matsayin waɗanda ake ƙara na farko zuwa na huɗu.

Mai Shari’ar ta amince da hujjar waɗanda ake ƙarar cewa El-Rufai ya riga ya shigar da makamantan ƙorafe-ƙorafe a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da kuma Babbar Kotun Tarayya.

Ta kuma bayyana cewa ba za a yi amfani da kotu wajen hana hukumomin tsaro da na bincike gudanar da ayyukan da doka ta ba su ba.

Abdulmalik ta bayyana ƙarar El-Rufai a matsayin wadda aka gina bisa hasashe, kuma ba ta da hujjar da za ta sa kotu ta amince da ita.

Ta ƙara da cewa ƙarar ba ta nuna wata hujja ta doka da za ta ba da damar shigar da EFCC, DSS da AGF cikin ƙarar ba, don haka ta cire sunayensu daga cikin waɗanda ake ƙara.

Ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/368/2026, lauyan El-Rufai, Oluwole Iyamu, wanda babban lauya ne mai mukamin SAN, ya shigar da ita a ranar 24 ga Fabrairu.

El-Rufai ya nemi kotun da ta hana waɗanda ake ƙarar ɗaukar matakin rufe asusun bankinsa ko ƙwace kadarorinsa har sai an kammala sauraron ƙarar ta asali.

Ya kuma nemi umarnin wucin gadi da zai tilasta wa waɗanda ake ƙarar ci gaba da barin al’amura yadda suke, domin hana ɗaukar matakin da zai zama ba za a iya sauya shi ba daga baya.

Tsohon gwamnan ya bada hujjar cewa kuɗin alawus ɗin sallama da ya karɓa bayan kammala wa’adin mulkinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023 ba za a iya zargin cewa kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya ba.

Ya kuma nemi kotun ta bayyana cewa kadarorin da ya saya da kuɗin alawus ɗin sallamar nasa ne bisa doka kuma ya mallake su bisa ƙa’ida.

Haka kuma, El-Rufai ya nemi umarnin dindindin da zai hana waɗanda ake ƙarar rufe asusun bankinsa, ƙwacewa ko karɓe kadarorinsa, ko kuma yin duk wani katsalandan ga kadarorinsa da kuɗaɗen da ke bankinsa.

Ya kuma nemi a biya shi diyyar Naira biliyan ɗaya, wadda ta haɗa da diyyar gama-gari da ta musamman, bisa zargin barazanar tauye masa haƙƙoƙinsa na asali, jefa shi cikin damuwa da tashin hankali, da kuma ɓata masa suna sakamakon barazanar ƙwace kadarorinsa ta hanyar da ya ce ba ta dace da doka ba.

Bugu da ƙari, ya nemi a biya shi Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin shari’a, ciki har da kuɗin lauyoyi da sauran kuɗaɗen da aka kashe wajen shigar da ƙarar.

A cikin ƙin amincewa da ƙarar, ICPC ta roƙi kotun da ta yi watsi da ita, tana mai cewa ba ta cika ƙa’idojin shari’a ba kuma babban misali ne na amfani da kotu ta hanyar da ba ta dace ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here