Atiku ya soki rage farashin man fetur na kwanaki 30 na gwamnatin tarayya

Former Vice President Atiku Abubakar 750x430

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki shirin Gwamnatin Tarayya na rage farashin man fetur na tsawon kwanaki 30 a gidajen man Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL).

A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa da Yaɗa Labarai na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Alhamis, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana matakin a matsayin na wucin gadi, wanda ba zai magance wahalhalun da tsadar man fetur ta jefa ’yan Najeriya a ciki ba.

Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za a fara aiwatar da ragin ne na tsawon kwanaki 30, inda aka ba masu harkokin sufuri na jama’a fifiko.

Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya ce wannan shiri na kwanaki 30 ba yana nufin dawo da biyan tallafin man fetur ba ne.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta bar NNPCL ya riƙa sayar da man fetur a farashin da ya saya ko ya samar da shi a lokacin.

Atiku ya bayyana shirin a matsayin wani matakin tallata gwamnati da aka yi cikin firgici, yana zargin gwamnatin da samar da sauƙin rayuwa na ɗan lokaci maimakon magance babbar matsalar tsadar rayuwa.

“Atiku ya yi watsi da wannan shirin tallafin man fetur na wucin gadi da aka tsara bisa kalandar siyasa da zaɓe. ’Yan Najeriya ba wawaye ba ne da za a rage musu farashin man fetur na wata guda bayan shekaru ana gallaza musu da tsadar farashi, sannan a sa ran za su manta da wahalhalun da suka sha da zarar rangwamen ya ƙare. Wannan abin kunya ne kuma rashin tausayi ne,” in ji shi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya tambayi abin da zai faru bayan kwanaki 30 ɗin, yana mai cewa ’yan Najeriya za su ci gaba da fuskantar tsadar man fetur, kuɗin sufuri da kayan abinci.

“Me zai faru a rana ta 31? ’Yan Najeriya za su tashi da safe su tarar da farashi iri ɗaya mai tsanani, kuɗin sufuri mai tsada da kuma ci gaba da tashin farashin abinci. Gwamnati ba za ta iya samar da sauƙin rayuwa na wata guda kawai ba, sannan ta sa ran ’yan Najeriya za su yaba mata alhali wahalhalun suna nan daram,” in ji shi.

Atiku ya kuma nuna shakku kan faɗin shirin, yana mai cewa za a aiwatar da shi ne kawai a gidajen mai na NNPCL. Ya ce har yanzu gwamnati ba ta bayyana adadin kuɗin da masu ababen hawa za su biya a kan kowace lita ta man fetur ba, ko kuma ta bayar da tabbacin cewa rangwamen da masu sufuri za su samu zai sa su rage kuɗin da suke karɓa daga fasinjoji.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi iƙirarin cewa matakin da gwamnati ta ɗauka na gabatar da wannan shiri na wucin gadi ya tabbatar da sahihancin shawarar da ya gabatar ta tallafa wa samar da man fetur da aka tace a cikin gida.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here