An kashe wasu ‘yan ƙasar Saudiyya uku, ciki har da wani kyaftin ɗin jirgin saman Saudia, a hare-hare biyu da aka kai Filin Jirgin Sama na Sarki Khalid da ke Riyadh a ranar Alhamis, a cewar hukumomin kula da harkokin jiragen sama.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ce ta bayyana adadin waɗanda suka mutu a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, inda ta ƙara da cewa wasu mutane da dama ‘yan ƙasashe daban-daban sun jikkata a hare-haren.
Read also: Trump ya fice daga tattaunawa bayan zargin ‘yar jarida da karya
A cewar hukumar, harin farko ya shafi wasu wurare a cikin filin jirgin, yayin da harin na biyu ya auka kan wani jirgin sama mallakin kamfanin Saudia, wanda shi ne babban kamfanin jiragen saman ƙasar.
Daga cikin waɗanda suka mutu akwai Kyaftin Hamoud Ali Alkalthami, wanda aka tabbatar da cewa yana cikin waɗanda harin ya rutsa da su.
GACA ta ce jami’an agajin gaggawa da sauran hukumomin da abin ya shafa sun ɗauki matakin gaggawa bayan faruwar lamarin, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci domin ba su kulawar lafiya.
Read also: Yadda bikin binne gawar Fafaroma ta kasance
Ta bayyana cewa raunukan waɗanda suka jikkata sun bambanta, daga masu sauƙi zuwa masu tsanani, yayin da hare-haren suka kuma haddasa lalacewar kadarori.
Hukumar ta ce tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tantance girman barnar da aka yi da kuma ɗaukar matakan da suka dace don kare fasinjoji, ma’aikatan filin jirgin da kuma kayayyakin aikin gudanar da sufurin jiragen sama na ƙasar.
GACA ta kuma tabbatar da cewa an ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama da gudanar da ayyukan filin jirgin bayan hare-haren.
(Xinhua/NAN)














































