Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta fara shari’a da dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Abba Kyari kan tuhumar safarar miyagun kwayoyi a babbar kotun tarayya, Abuja.
Hukumar ta gabatar da kwamandan miyagun kwayoyi (sashin bincike), Patricia Afolabi, domin ta ba da shaida ta farko a gaban mai shari’a Emeka Nwitw, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Shaidar ta faɗa wa Kotu cewa aikinta a hukumar NDLEA ya ƙunshi karba da kuma gudanar da bincike kan abubuwan da suka shafi miyagun kwayoyi.
Ta sanar da Kotu cewa a ranar 7 ga watan Fabrairu, 2022, jami’in hukumar, Abubakar Aliyu, ya kawo mata wani Fakiti da ake ganin abun da ke ciki ɗauke da kulli 24 a ciki.
A jawabin da ta yi wa Kotu, ta ce kowane ƙulli na dauke da wani abu fari mai nauyin giram 0.5grams, kamar yadda Leadership ta ruwaito. Shaidar ta ƙara da zayyana wa Kotun cewa fakitin da aka kawo mata ya kunshi takarda wato Fom ɗin bukatar gudanar da bincike kan abubuwan da ke ciki.













































