Hukumomi a ƙaramar hukumar Dala da ke Jihar Kano sun kama wani mutum mai shekaru 30, mai suna Habibu Abdullahi, bisa zargin samar da takardun shaidar asali na bogi, watanni bayan wani binciken jaridar SolaceBase ya bankado yadda ake samun takardun ta hanyar biyan kuɗaɗen da ba bisa ƙa’ida ba tare da kauce wa tantancewa yadda ya kamata ba.
An ruwaito cewa an kama Abdullahi, wanda ke gudanar da shagon buga takardu a unguwar Kurna da ke ƙaramar hukumar Dala, a ranar 13 ga Oktoban 2026, bayan gano wata takardar shaidar asali da ake zargin ta bogi ce, wadda wani mutum ya gabatar domin samun wani aiki na hukuma.
Read also: Kotu ta yi watsi da karar Ighodalo, ta tabbatar da nasarar Okpebolo
A cewar wata sanarwa da ƙaramar hukumar ta fitar a ranar Litinin, wani jami’in ofishin bayar da takardun shaidar asali, Yahya Musa Jibrin, ya ce an gano cewa takardar bogi ce yayin tantance ta. Hakan ya sa jami’an suka tuntuɓi hukumomin tsaro domin gudanar da bincike kan inda takardar ta fito da kuma gano wanda ake zargin ya samar da ita.
Jibrin ya ce binciken ya kai ga Abdullahi, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi kafin a miƙa shi ga ’yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
Daga bisani, an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, wadda ta bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali yayin da ake ci gaba da bincike.
An kama mutumin ne watanni bayan da SolaceBase ta bankado yadda ake zargin ana samun takardun shaidar asali a ƙaramar hukumar Dala ta hanyar biyan kuɗaɗen da ba bisa ƙa’ida ba, tare da kauce wa matakan tantancewa da doka ta tanada.
Read also: Wata babbar mota ta murkushe mutum 2 har lahira a Kano- FRSC
A wani rahoton bincike da ta wallafa a ranar 26 ga Afrilun 2026, mai taken “Yadda jami’ai a wata ƙaramar hukuma a Kano suka mayar da takardun shaidar asali hanyar karɓar cin hanci,” SolaceBase ta bayyana yadda wasu masu shiga tsakani ke taimakawa wajen samar da takardun ta hanyar karɓar kuɗi daga Naira 2,000 zuwa Naira 10,000.
A yayin gudanar da binciken sirri, SolaceBase ta samu takardar shaidar asali ga wani mutum daga Jihar Sakkwato bayan biyan Naira 8,000, ba tare da kammala matakan amincewa da tantancewa da ake buƙata ba.
Binciken ya kuma nuna damuwa kan yiwuwar amfani da irin waɗannan takardu wajen samun ayyukan gwamnati, tallafin karatu, damar neman ilimi da sauran alfanun da aka tanada musamman ga ’yan asalin wuraren da abin ya shafa.
Yayin da binciken da aka gudanar a baya ya fi mayar da hankali kan zarge-zargen rashin bin ƙa’ida wajen bayar da takardun shaidar asali, kamen da aka yi yanzu ya shafi zargin samar da takardun bogi a wajen tsarin hukuma.
Da yake mayar da martani kan kamen, shugaban ƙaramar hukumar Dala, Malam Suraj Ibrahim Imam, ya ce ƙaramar hukumar a shirye take ta taimaka wa mutanen da ke nema ta halastacciyar hanya.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da karya doka zai fuskanci shari’a da ta dace.
Read also: Wani da ake zargi da kwacen waya ya kashe babban soja a Kaduna
Ya buƙaci mazauna yankin da su bi hanyoyin da doka ta tanada tare da ba hukumomin da abin ya shafa haɗin kai domin kare sahihancin takardun hukuma.












































