Daukar Ma’aikata: Hukumar Kwastam za ta sake binciken koke-koken masu neman aiki 397 da aka cire

BASHIR ADEWALE ADENIYI Customs 750x430

Hukumar Hana Fasa Ƙwaurita Ƙasa (NCS) ta sanar da shirin sake duba korafe-korafen wasu masu neman aiki da aka cire yayin tantancewar daukar sabbin ma’aikata, duk da cewa sunayensu sun bayyana cikin jerin waɗanda aka zaɓa domin horo.

Hukumar ta ce Kwanturola Janar na Kwastom, Bashir Adewale Adeniyi, ne ya bayar da umarnin sake duba kowanne ƙorafi, bayan ganawa da wasu daga cikin masu neman aikin da suka nuna rashin gamsuwa da matakin da aka ɗauka a kansu.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Mataimakin Kwanturolan Kwastam, Abdullahi Maiwada, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, hukumar ta bayyana cewa manufar sake duba korafe-korafen ita ce tabbatar da cewa an binciki masu inganci, tare da kiyaye sahihancin tsarin daukar ma’aikata.

Hukumar ta bayyana cewa kasancewar sunan mai neman aiki a cikin jerin sunayen waɗanda aka zaɓa a matakin ƙarshe ba yana nufin an tabbatar da ɗaukar shi aiki kai tsaye ba.

Ta ce ana buƙatar su bi matakai daban-daban na tantancewa, waɗanda suka haɗa da binciken takardun shaidar karatu, gwajin ƙarfin jiki, binciken lafiya, tabbatar da shekaru da kuma gwajin amfani da miyagun ƙwayoyi.

A cewar hukumar, an gano kura-kurai a tsarin tantance masu neman aiki 397, waɗanda suka shafi amfani da miyagun ƙwayoyi, ƙarfin jiki, bayanan lafiya, shekaru da takardun da aka gabatar.

Ta ƙara da cewa an kuma cire wasu sakamakon gano wasu kura-kurai a tsarin zaɓen su.

Hukumar Kwastam ta buƙaci masu nemab aikin da abin ya shafa, waɗanda suke ganin an cire su ba bisa ƙa’ida ba, da su aika bayanansu da korafe-korafensu zuwa adireshin imel ɗin [email protected] domin a sake duba lamarinsu.

Ta ce za a sake tantance masu neman da ke buƙatar a sake duba matsayinsu, tana mai jaddada cewa sake tantancewar ba yana nufin za a ba su damar shiga kwalejin horaswa kai tsaye ba.

Hukumar ta kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da hannu a aikata laifuka, ciki har da yin jabun takardun shaidar karatu da sauran laifuffuka, za a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar matakin shari’a da gurfanar da shi a gaban kotu.

A ƙarshe, hukumar ta buƙaci masu neman da abin ya shafa da sauran jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da amfani da hanyar da aka tanada wajen miƙa korafe-korafensu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here