Majalisar Kano ta gayyaci dan majalisa kan bidiyon da bai dace ba a kafar sada zumunta

Kano State House of Assembly 700x430

Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta gayyaci wani ɗan majalisa, Yusuf Bello Aliyu na Nassarawa, kan wasu kalamai da zarge-zargen cin mutunci da suka yaɗu a kafafen sada zumunta.

Ana sa ran Bello Aliyu zai gurfana a gaban Kwamitin Da’a na majalisar a ranar Talata.

Kakakin majalisar, Jibril Ismail-Falgore, ne ya sanar da matakin yayin zaman majalisar na ranar Litinin, bayan wani ƙudiri na gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar Minjibir, Abdulhamid Abdul-Minjibir, ya gabatar.

Abdul-Minjibir ya ce ya ga wani saƙo da ɗan majalisar ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda yake riƙe da kunnuwan zomo tare da furta kalaman da ba su dace da matsayin ɗan majalisa mai girma ba.

“Batun da nake son gabatarwa ya shafi wani saƙo da na gani a kafafen sada zumunta, wanda abokin aikina mai wakiltar ƙaramar hukumar Nassarawa ya wallafa, inda yake riƙe da kunnuwan zomo tare da furta kalaman da ba su dace da matsayin ɗan majalisa mai girma ba.

“Taken ‘Honorable’ matsayi ne na musamman da ya kamata a mutunta. Ya kamata mu riƙe shi cikin mutunci, mu kuma yi abubuwan da suka dace domin samun kyakkyawan suna.

“Duk wani ɗan majalisa da ya ga wannan saƙo zai ji matuƙar damuwa.

“Ni kaina na damu matuƙa da wannan saƙo, shi ya sa na ga ya dace in sanar da majalisar domin a mayar da batun ga Kwamitin Da’a, ya gayyaci ɗan majalisar domin ya yi bayani kan yanayin da ya kai shi ga yin hakan. Hakan zai zama darasi ga sauran mutane,” in ji Abdul-Minjibir.

Shi ma da yake magana kan lamarin, Dr Musa Ali Kachako na Takai, ya ce ya kamata ’yan majalisa su zama abin koyi ga sauran al’umma.

Ya buƙaci majalisar da ta ɗauki matakin ladabtarwa bisa tanade-tanaden dokoki da ƙa’idojin gudanar da ayyukanta, domin jama’a su fahimci cewa “su masu tsara dokoki ne, ba masu karya dokoki ba.”

A nasa ɓangaren, Usman Abubakar Tasiu na Kiru, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ba ta dace ba, musamman wajen cin mutuncin wasu.

Ya jaddada buƙatar samar da wata doka da za ta daidaita yadda ake amfani da kafafen sada zumunta.

Sai dai Kakakin majalisar ya mayar da batun ga Kwamitin Da’a na majalisar, inda ya umarce shi da ya gayyaci ɗan majalisar da abin ya shafa domin ya bayyana a gabansa ranar Talata.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here