Tinubu ya tsawaita wa’adin shugabannin NIS da NCoS

MixCollage 19 Oct 2026 09 38 PM 1806 1792442349 1200x630 1 750x430

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya amince da tsawaita wa’adin shugabar Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), Kemi Nandap, da watanni 18, inda wa’adinta zai ƙare a ranar 30 ga Yunin 2028.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya sanar da tsawaita wa’adin a ranar Litinin.

Haka kuma, Tinubu ya amince da tsawaita wa’adin shugaban Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS), Sylvester Ndidi Nwakuche, da watanni 18, inda wa’adinsa zai ƙare a ranar 26 ga Mayun 2028.

Sanarwar ta ce amincewar ta biyo bayan shawarar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji Ojo, ya bayar domin magance gibin da ka iya tasowa wajen maye gurbin shugabannin hukumomin biyu, tare da ba kwamitocin gudanarwarsu damar naɗa sababbin shugabanni.

A cewar sanarwar, Shugaban Ƙasar ya yaba wa shugabannin hukumomin biyu bisa sauye-sauyen da suka samu nasarar aiwatarwa a ƙarƙashin jagorancinsu, tare da buƙatar su ƙara ƙaimi wajen bunƙasa nasarorin da aka samu.

Tinubu ya zaɓi Nandap a matsayin Shugabar Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa a ranar 21 ga Fabrairun 2024, kafin daga bisani Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nata a ranar 1 ga Maris ɗin 2024.

Shi kuwa Nwakuche, an zaɓe shi domin jagorantar Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa a watan Disamba na 2024, sannan Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗinsa a watan Maris na 2025.

SolaceBase ta ruwaito a watan Maris na 2025 cewa Tinubu ya amince da tsawaita wa’adin Nandap har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2026.

Nandap, wadda ta shiga aikin Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa a ranar 9 ga Oktoban 1989, an naɗa ta Shugabar hukumar a ranar 1 ga Maris ɗin 2024, kuma ana sa ran za ta yi ritaya a ranar 31 ga Agustan 2025.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here