Jigawa ce kan gaba wajen gurfanar da wadanda ake tuhuma da yin fyaɗe- Dakta Musa Adamu Aliyu SAN

ICPC Boss

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifukan aikata zamba ta Najeriya (ICPC), Dakta Musa Adamu Aliyu SAN, ya ce jihar Jigawa ce ta fi kowace a Najeriya wajen gurfanar da mutanen da ake zargi da aikata fyade a lokacin da yake rike da mukamin kwamishinan shari’a.

Aliyu ya bayyana haka ne a baya-bayannnan yayin wani taron tattaunawa a taron da kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) suka shirya don marabtar sabbin lauyoyin wanda aka gudanar a Sakatariyar NBA da ke Abuja.

A cewarsa, babu wata jiha a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023 da ta ke da yawan mutanen da ake tuhuma da shari’o’in fyade da kamar jihar ta Jigawa.

Bugu da kari, Dr. Aliyu ya kra da cewa da yawa daga cikin wadannan kararraki, musamman na kotun daukaka kara, an rubuta su kuma an gabatar da su.

Baya ga yadda aka rika gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, ya ce lokacin ya samar da sauye-sauye a fannin shari’a, wadanda sun hada da zartar da dokar kare hakkin yara da dokar kare al’umma a jihar Jigawa.

Yayin da yake rike da mukamin Dr. Aliyu ya rika bayyana a gaban kotu, inda yake tafiyar da al’amuran da suka shafi farar hula da na laifuka a matakin shari’a da daukaka kara.

Ya bayar da misali da shigarsa cikin karar da wasu manyan lauyoyin jihohi suka shigar da gwamnatin tarayya kan manufar sauya fasalin takardun kudi na Naira a matsayin misali na yadda ya ke gudanar da harkokin shari’a.

SolaceBase ta ruwaito cewa kalaman Dr. Aliyu na da nufin karfafa gwiwar matasan lauyoyi da su dauki aikin hidimta wa al’umma a matsayin hanyar da za ta iya yin tasiri na gaske, duk da kalubalen da ke tattare da bangaren.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here