Jami’ar Katsina ta kori ɗalibai 57 bisa maguɗin Jarrabawa

Uni Jos Students

Majalisar gudanarwa ta jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina, ta amince da korar dalibai 57, bisa samun su da laifin tafka maguɗin jarrabawa.

Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Asabar, ta hannun Hajiya Fatima Sanda, shugabar yada labarai da tsare-tsare ta jami’ar.

A cewar sanarwar, shawarar ta zo ne a yayin taron majalisar gudanarwar karo na 125 biyo bayan shawarwarin da kwamitin da’a na harkokin jarrabawar jami’ar (UCEMC) ya bayar.

Haka kuma sanarwar ta ce, kafin ɗaukar matakin, kwamitin ya yi bincike a kan laifukan da suka shafi bangarori da dama.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, an yi wa wasu dalibai biyar hukuncin maimaita aji na tsawon zango biyu a shekarar karatu ta 2024/2025, tare da soke takardun jarrabawar da abun ya shafa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wasu ƙarin ɗalibai biyu sun samu rubutaccen gargadi a hukumance, wanda yanzu haka suna kan bayanan karatun su na dindindin.

A cikin sanarwar, jami’ar ta UMYU ta jaddada cewa, matakan sun nuna manufarta ta rashin ɗaga ƙafa ga masu nuna rashin da’a, inda ta kara da cewa an yi hakan ne domin ya zama izina ga wasu ɗaliban.

“UMYU ta ci gaba da jajircewa wajen kiyaye martabar ka’idojinta na ilimi kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani abu da zai kawo cikas ga sahihancin jarrabawarta.”

Sanarwar ta ce, “An bukaci dalibai da su bi ka’idojin ilimi sosai tare da kauce wa yin duk wani nau’i na munanan dabi’u, do kuwa ba za ta saurara wa duk ɗalibin da ta samu da aikata laifi ba.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here