Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ta sanar da rufe babbar kofar shiga tsohuwar jami’ar na wucin gadi don yin gyare-gyare, daga ranar 13 ga Maris, 2025.
A cewar wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a na jami’ar kuma mataimakin magatakarda Lamara Garba ya fitar a ranar Lahadi, ta ce matakin wani bangare ne na kokarin da jami’ar ke ci gaba da yi na inganta ababen more rayuwa da kuma inganta ayyukan ta.
Ya bukaci ma’aikata, dalibai, da masu ziyara da su yi amfani da wata kofar a madadin kofar da aka rufe yayin da ake aikin gyarawa.
Karin labari: Jami’ar Bayero ta kori dalibai 62, ta hukunta wasu 17
Jami’ar ta bayar da hakuri kan duk wata matsala da rufewar za ta haifar, inda ta tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa ana kokarin kammala aikin cikin gaggawa.