Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta ƙasa, JAMB, ta gudanar da jarabawar ƙarin matsayi ta na’ura mai Ƙwaƙwalwa ga ma’aikatan da suke matakin Daraktoci 6,000 ƙarƙashin hukumar ayyukan gwamnati ta tarayya.
Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa an gudanar da jarabawar ne a birnin Abuja, tare da wasu ma’aikata a ƙasashen Birtaniya, Amurka, Indiya da Masar.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin sabon salo mai ƙarfi wajen amfani da fasahar zamani domin inganta gaskiya da inganci a tsarin ƙarin girma ga ma’aikatan gwamnati.
Farfesa Oloyede ya bayyana cewa tsarin jarabawar ta na’ura mai Ƙwaƙwalwa an tsara shi ne cikin sauƙi, inda duk wanda ke iya amfani da wayar hannu zai iya rubuta jarabawar cikin sauƙi.
Ya kuma ce wannan tsari na nuna ƙwarewar hukumar wajen gudanar da jarabawa ta gaskiya ta amfani da fasaha a sassa daban-daban na gwamnati.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage tsoron da ma’aikata ke ji kan amfani da na’ura mai Ƙwaƙwalwa a jarabawarsu, domin da dama daga cikinsu sun fara nuna kwarin gwiwa bayan sun gane yadda tsarin ke tafiya cikin sauƙi da fahimta.
Farfesa Oloyede ya yaba wa hukumar ayyukan gwamnati ta tarayya saboda haɗin kai, yana mai cewa amfani da na’ura mai Ƙwaƙwalwa a jarabawa zai ƙara sahihanci da rage yin magudi a cikin tsarin ƙarin girma ga ma’aikata.
Haka kuma kwamishinan hukumar da ke wakiltar Babban Birnin Tarayya da Jihar Neja, Dakta Hussaini Adamu, ya nuna gamsuwa da yadda aka gudanar da jarabawar, yana mai cewa tsari ne mai tsafta da sauƙin fahimta.
Shi ma shugaban hukumar ayyukan gwamnati ta tarayya, Farfesa Adetunji Olaopa, ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko da hukumar za ta yi amfani da tsarin jarabawar ta na’ura mai Ƙwaƙwalwa wajen ƙarin girma ga ma’aikata.
Ya ce wannan ci gaba ne mai muhimmanci wajen sabunta tsarin tantance ma’aikata, tare da samun tabbaci daga JAMB wajen gudanar da aikin cikin fasaha.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa akalla cibiyoyi 10 a fadin Babban Birnin Tarayya ne aka yi amfani da su wajen gudanar da jarabawar.













































