Hukumomin Saudiyya sun buƙaci Musulmi su fara duba sabon watan Dhu Al-Hijjah

Sabon, watan, Al-Hajji, hukumomi, saudiyya, duba, musulmi
Hukumomin Kasar Saudiyya sun buƙaci al'ummar Musulmi a faɗin ƙasar su fara duban watan Dhu Al-Hijjah daga gobe Alhamis da yamma, domin tsayar da ranar Babbar...

Hukumomin Kasar Saudiyya sun buƙaci al’ummar Musulmi a faɗin ƙasar su fara duban watan Dhu Al-Hijjah daga gobe Alhamis da yamma, domin tsayar da ranar Babbar Sallah.

Gobe Alhamis za ta kasance, ranar 29 ga watan Dhu al-Qadah shekara ta 1445 bayan Hijrah, daidai da 6 ga watan Yuni, 2024.

A wata sanarwa da Kotun ƙolin kasar ta fitar ta ce, “Idan Juma’a 7 ga watan Yuni ta tabbata, ranar farko ta Dhu Al-Hijjah, Babbar Sallah za ta kasance ranar Lahadi 16, ga watan Yuni kenan.”

Karin labari: An zargi wata sabuwar Amarya da yanke al’aurar mijinta a Kaduna

Babbar Sallah dai na kasancewa ne ranar 10 ga watan Dhu Al-Hijjah, wanda shi ne wata na karshe wato na 12 na Hijirar Annabi Muhammad (S.A.W).

Kotun ta buƙaci ɗaiɗaikun mutane da za su iya duba sabon watan, da idanuwansu ko kuma da madubin hangen nesa da su je wata cibiya mafi kusa da su domin taimaka musu zuwa ga kotu mafi kusa domin su bayar da bayani idan har sun ga sabon watan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here