Hukumar kula da ƴan Sanda ta tantance sama da manyan jami’ai 500 don ƙara musu matsayi

Senior Police Officers 750x430 (1)

Hukumar kula da ’yan sanda ta ƙasa ta fara tantance sama da manyan jami’an ’yan sanda 500 daga fadin ƙasar nan a ranar Alhamis domin cancantar samun ƙarin matsayi.

Daga cikinsu akwai manyan sifeton ƴan sanda 56 da za a ɗaga su zuwa mataimakan kwamishinonin ’yan sanda.

Haka kuma, sifetoci 451 aka gabatar don ɗaga su zuwa manyan sifetocin ’yan sanda.

Jami’an da aka tantance sun rubuta jarabawa ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Paul Adamu Galumje, wanda ke wakiltar bangaren shari’a a hukumar, tare da Taiwo Lekanu, kwamishina mai kula da harkokin ’yan sanda a hukumar.

Mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya ce daga yanzu hukumar za ta ɗauki jarabawar ƙarin girma a matsayin muhimmin sharadi kafin a ɗaga matsayin jami’an.

Karin labari: Zargin Zamba: Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon Ministan Wutar Lantarki

Ya ce hakan na da muhimmanci domin tabbatar da cewa ’yan sanda sun shirya da basira wajen fuskantar ƙalubalen tsaro na ƙarni na 21 bisa tsarin aiki na ƙasashen duniya.

Ana kuma sa ran mataimakan sifetocin ’yan sanda za su bayyana gaban hukumar a ranar Juma’a, 19 ga Satumba, domin yin tasu jarabawar.

Shugaban hukumar, mataimakin babban sufeton ’yan sanda mai ritaya, Hashimu Argungu, ya bayyana cewa hukumar na ƙoƙarin samar da rundunar ’yan sanda ta zamani da za ta dace da sabuwar Najeriya da gwamnati ke ginawa.

Ya ce hukumar ba za ta huta ba har sai an cimma wannan buri, tare da kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan rundunar yan sanda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here