Hukumar kashe gobara ta tarayya ta mikawa ‘yan sanda direban mota bayan faruwar hadari a Abuja, ta dakatar da wasu ma’aikata

Federal Fire Service (1)

Hukumar kashe gobara ta tarayya ta mikawa ‘yan sanda direban wata motar ceto da ya haddasa hatsarin da ya faru a daren Juma’a a Wuse 2, Abuja, tare da dakatar da jami’an da ke bakin aiki a wannan rana har sai an kammala bincike.

Mummunan hatsarin wanda ya auku da misalin karfe 11:00 na ranar Juma’a a unguwar Wuse da ke babban birnin tarayya Abuja, ya yi sanadin mutuwar wasu matasa uku tare da jikkata mutum daya.

Hatsarin ya faru ne a lokacin da motar kashe gobara ke dawowa don cika tankin ruwanta bayan da ta amsa kiran gobarar da ta tashi a Avenue Plaza, Banex.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, babban jami’in hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya Abuja, Momodu Ganiyu, ya bayyana lamarin a matsayin mai ratsa zuciya, inda ya amince da rashu mara misaltuwa da iyalan mamatan suka yi.

“A matsayinmu na ma’aikata, mun yi nadama kan lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu matasa uku, mun san cewa lokaci ne mai wahala ga iyalansu su shawo kan lamarin, idan aka yi la’akari da yawan shekarun yaran da wannan hatsarin ya rutsa da su.

Karanta: NDLEA ta kama wata mata ‘yar kasar Iran da take dauke da hodar iblis a cikin sirri a filin jirgin sama

Hukumar kashe gobara ta Tarayya tana sane da cewa rasa ’ya’yan mutum abu ne mai raɗaɗi wanda ke nuna babban canjin rayuwar iyali kuma ya ƙunshi ɓacin rai da yawa, ”in ji shi.

Ya ce daya daga cikin motocin dakon ruwa da ya dawo ya cika ruwan ya yi karo da wata mota kirar Toyota Camry a unguwar Wuse.

Rahotanni sun ce motar ta fito ne daga kan titin da ke hadewa a lokacin da hadarin ya afku.

Ganiyu ya kuma bayyana cewa, Kwanturola Janar din ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Ya kara da cewa direban motar kashe gobarar yana hannun ‘yan sanda a halin yanzu, yayin da aka dakatar da ma’aikatan cibiyar ceto da ke babban birnin tarayya Abuja har sai an kammala bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here