Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun kashe mutane bakwai a lokacin da suka kai hari kauyen Magajin-Wando da ke ƙaramar hukumar Dandume.
Kwamishinan tsaro na cikin gida, Dr. Nasir Mu’azu, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa.
Ya ce harin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na dare, inda ƴan bindigar suka yi ƙoƙarin kashe mutane da dama, amma saurin shigowar rundunar Community Watch Corps (CWC) ya taimaka wajen fatattakar su, wanda ya rage tsananin asarar rayuka.
Sai dai a yayin da ake jigilar waɗanda suka ji rauni zuwa asibiti, ƴan bindigar da suka rarrabu suka sake kai musu hari, inda a wannan karo, aka yi musayar wuta, motar CWC ta ƙone, amma jami’an sun yi nasarar tsira.
Kwamishinan ya bayyana cewa binciken farko ya nuna harin ramuwar gayya ne daga ƴan ta’addan saboda mutanen su da aka kashe a baya, ya kuma yaba da jarumtaka da jajircewar CWC wajen kare al’umma duk da haɗarin da ke tattare da hakan.
Gwamnati ta mika ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ’yan uwa tare da fatan samun waraka ga waɗanda suka ji rauni.
Haka kuma, ta jaddada cewa za ta ƙara ƙaimi a yaƙin da ake yi da ƴan ta’adda tare da haɗin gwiwar sojoji, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro.
Mu’azu ya kuma bukaci jama’a da su kasance masu sa ido da bayar da bayanai ga hukumomin tsaro domin tallafa wa aikin kawar da barazanar tsaro a jihar.













































