Gwamnatin Kano ta raba karin murahun girki na zamani 1,500 ga mata

FB IMG 1792406658498 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta raba murahun girki na zamani guda 1,500 ga mata masu karamin karfi a fadin jihar, a mataki na biyu na shiri da aka tsara domin rage gurbatar muhalli, dakile sare bishiyoyi da kuma kare iyalai daga illolin lafiya da hayakin itacen girki ke haifarwa.

SolaceBase ta rawaito cewa Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru M. Hashim ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin.

Hashim ya ce rabon murahun na daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na inganta dorewar muhalli, rage gurbatar iska da kuma kare mata da iyalansu daga illolin hayakin da ake samu yayin amfani da hanyoyin girkin gargajiya.

“A yau, mun gudanar da mataki na biyu na rabon murahun girki na zamani, inda muka raba karin 1,500 ga mata masu karamin karfi a fadin Jihar Kano.”

Ya bayyana cewa an tsara shirin ne domin rage sare bishiyoyi, inganta ingancin iska da kuma kare lafiyar mata da iyalansu, wadanda galibi ke fuskantar hayakin itacen girki yayin da suke amfani da shi.

Kwamishinan ya nuna godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa wajen yaki da sauyin yanayi da kuma tallafa wa masu karamin karfi a matakin al’umma.

A cewarsa, gwamnan ya hada rabon murahun girkin da tallafin kudi na Naira 25,000 ga kowane mai cin gajiyar shirin, domin taimaka mata wajen gudanar da kananan sana’o’i da inganta rayuwa.

Hashim ya ce an samar da karin tallafin ne domin tabbatar da cewa shirin ba wai kawai zai magance matsalolin muhalli ba ne, har ma ya taimaka wajen rage kalubalen tattalin arziki da mata masu karamin karfi ke fuskanta.

Wannan karin rabon murahu ya biyo bayan kaddamar da shirin samar da murahun girki na zamani da gwamnatin jihar ta yi a watan Satumba, lokacin da ta fara rabon 3,400 da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta ware wa Jihar Kano.

SolaceBase ta rawaito cewa a lokacin kaddamar da shirin a ranar 27 ga Satumban2026, Hashim ya bayyana cewa an riga an raba murahu kusan 800 ga mata masu karamin karfi, inda kowacce ta kuma ta samu tallafin Naira 25,000 daga gwamnatin jihar domin karfafa sana’arta da inganta rayuwarta.

Shirin na daga cikin manyan kokarin da ake yi na rage dogaro da itacen girki, dakile gurɓatar muhalli da kuma bunkasa amfani da hanyoyin girki masu tsafta a fadin jihar.

Ana sa ran gwamnatin za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suka hada da kare muhalli da karfafa tattalin arziki, musamman ga mata da sauran masu karamin karfi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here